Ndume Ya Gargadi Mazauna Maiduguri Bayan harin Bam-Bam daya kashe mutane 23

Sanata Mohammed Ali Ndume, wanda ke wakiltar Borno South, ya yi tir da harin bam-bam da ya girgiza Maiduguri a daren Litinin, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 23 da raunata 146.
A cikin wani jawabi da ya sanya hannu da kansa, Ndume ya bayyana harin a matsayin “mummuna da rashin jin kai,” inda ya ce an kai hari ne a wurare masu cunkoso, ciki har da Monday Market da jami,ar Maiduguri Teaching Hospital (UMTH).
Sanatan, wanda ke gudanar da Umrah a Saudi Arabia, ya nuna bakin cikin sa sosai kan wannan al’amari tare da jaddada kudurinsa na ganin an kara inganta tsaro a Borno da kasa baki daya. Ya ce dole ne a magance barazanar da ke addabar rayukan fararen hula da gaggawa da hadin gwiwar hukumomi.
Ndume ya mika ta’aziyya ga Gwamnan Jihar Borno, Prof. Babagana Umara Zulum, iyalan wadanda suka rasa rayukansu, wadanda suka ji rauni, da kuma shugabannin Monday Market da UMTH, inda ake bai wa raunattun mutane magani.
Ya yaba da gaggawar daukar mataki daga hukumomin tsaro, tare da kara jan hankalin su wajen tsare rayuka da hana sake faruwar hare-hare.
“Ina kira ga mazauna Maiduguri, musamman a Borno South, da su kasance masu lura, su rika bayar da rahoto kan duk wani abu da ba na al’ada ba. Kada mu sassauta tsaro a wannan lokaci na musamman,” in ji Ndume.
Ya kuma yi addu’a domin samun rahama ga wadanda suka rasa rayukansu, ya warkar da raunattun cikin gaggawa, da samun zaman lafiya mai dorewa a Borno da Najeriya baki daya.





