LabaraiWassanni

Nijeriya ta naɗa Finidi George sabon kocin Super Eagles

Kwamitin gudanarwar Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya, NFF, ya amince da naɗa toshon ɗan wasan Nijeriya Finidi George a matsayin sabon kocin tawagar maza ta ƙasar, Super Eagles.

A yau Litinin ne kwamitin gudanarwa na Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya, NFF, ya karɓi shawarar kwamitin ƙwararru na hukumar, don naɗa Finidi George mai shekara 52, a matsayin sabon babban kocin tawagar maza ta ƙasar, Super Eagles.

Finidi George tsohon ɗan wasan Super Eagles ne da ke buga wasa a gaba. Ya kwashe watanni 20 a matsayin mataimakin tsohon koci Jose Peseiro, kafin ɗan Portugal ɗin ya ajiye aiki bayan kammala gasar kofin Afrika ta AFCON.

Bayan tafiyar Peseiro, Finidi ne ya ci gaba da riƙe ƙungiyar a matsayin babban koci na riƙo, inda ya jagoranci tawagar a wasanni biyu na sada-zumunta da ta buga a Maroko a watan jiya.

A wasannin biyu, Finidi ya jagoranci Super Eagles suka yi nasara kan tawagar Black Stars ta Ghana da ci 2-1. Sai dai a wasansu da Mali, sun yi rashin nasara da ci 0-2.

Finidi George yana cikin shahararriyar tawagar Nijeriya da ta ci kofin ƙasashen Afirka na shekarar 1994, wadda aka buga a Tunisia, sannan suka yi bajinta a karon farko da Nijeriya ta je gasar cin kofin duniya da aka yi a wannan shekarar a Amurka.

Ɗan wasan ya buga wa Nijeriya wasa har sau 62 inda ya je gasanni biyu na kofin duniya a 1994 da 1998. Sannan ya ciyo lambar yabo a gasannin kofin Afrika da aka buga a shekarun 1992, da 1994, da 2000, da 2002.

Lokacin yana ganiyarsa, Finidi ya buga wa manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Turai kamar Ajax Amsterdam, ta Netherlands, da Real Betis ta Sifaniya. A gida Nijeriya kuwa, ya buga wa Calabar Rovers da Sharks FC.

Babban aikin da ke gaban sabon kocin shi ne horar da Super Eagles ta shirya wa wasan neman gurbi a gasar kofin duniya ta 2026, inda Nijeriya za ta kara da Afirka ta Kudu, da kuma Benin a birnin Uyo da kuma Abidjan, nan da makonni biyar.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker