Ana Tuhumar Amal Umar Bisa Yunkurin Bada Cin Hanci
Hakan ya biyo bayan taron manema labarai da hukumar ‘yan sanda ta kira a jihar Kano, domin gabatar da wata jarumar fina-finan Hausa ta masana’antar kannywood wanda aka fi sani da Amal Umar, mai shekara ashirin da hudu wadda take zaune a jahar Kano.
A tattaunawarda akayi da wani jami’in dan sanda ya bayyana cewa hukumar ‘yan sandan ta gurfanar da ita ne a gaban kotu domin yunkuri na bada cin hanci da tayi ga ASP Salisu Ujama, wanda yake bincike akan wani Case na damfara da saurayinta, wanda ita ta fada cewa saurayinta neh yayi damfara. Akwai kudinda ya karba a hannun wani Alh. Yusuf Adamu, kimanin naira miliyan arba’in da nufin cewa zasuyi kasuwancin waya, daga nan sai ya gudu ba’a kara ganinsa ba.
Jami’in ya bayyana cewa lokacinda shi mai girma mataimakin shugaban ‘yan sanda na Najeriya wato AIG Muhammad Sanda a AIG zone 1 headquarters, ya samu petition daga HIDG Chambers wanda yake cewa sunfito kawo korafi neh domin a bincike wancan mutumin wanda ya gudu da naira miliyan arba’in.
Ya kara da cewa “Koda ‘yan sanda suka fara bincike sai suka gano cewa ya tura naira miliyan goma sha uku a asusun banki na wata mai suna Amal Umar. Sannan bincikensu yanuna musu cewa ‘yar wasan Hausa ce ta masana’antar kannywood.
Daga nan aka gayyace ita Amal Umar zuwa ofishin ‘yan sanda domin tazo tayi bayanin wannan kudi da aka gani acikin account nata, inda ta mika wuya take cewa lallai wannan kudin saurayinta ne ya tura mata.
Bayan anbada ita beli sai taje kotu ta nemi cewa kotu ta dakatar da ‘yan sanda daga wannan bincike da sukeyi akanta.
Bayan andakatar da bincike, dama lokacinda tazo nafarko tazo da motarta, motar tana nan a shalkwatan ‘yan sanda na zone 1. Da tadawo tanaso abata motarta sai tayi yunkurin bada cin hanci ga ASP Salisu Ujama, na naira dubu dari biyar domin yayi hakuri ya kashe wannan magana kuma abata motarta ta tafi da ita.
Jami’in yaci gaba da cewa a hukumance a aikin ‘yan sanda bazamu gurfanar dashi babu kwakkwarar shaida ba. Akan haka ne yace ta bashi dubu dari biyu da hamsin cewa zataje ta dawo ta bada cikon dubu dari biyu da hamsin.
Sannan ya tabbatar da cewa ASP Salisu Ujama ya karbi wannan kudi naira dubu dari biyu da hamsin, Kuma angurfanar da ita Jarumar agaban kotu domin tayi yunkurin bada cin hanci ga ‘yan sanda. Wannan abinda yafaru kenan shiyasa muka gayyace manema labarai domin muyi musu bayani, cewar shi jami’in.
Daga karshe yace zasu cigaba da wannan bincike kuma duk bayani da yakamata ayi wa al’umah, za’ayi musu.