KasuwanciLabarai

KEDCO Ta Karyata Labarin Cewa Zata Rika Chajin Magidanta 27,000 A Katsina

A rahoton da Fact24 ta wallafa acikin harshen hausa ta hanun Isma’il Nasir yana cewa Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na KEDCO, ya karyata labarin da ke yawo cewa Kamfanin zai rika Chajin Magidanta kudin bill har tsabar Kudi naira 27,000 a kowane wata a Katsina.

Wannan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Babban Jami’in Yada Labaru na Kamfanin Ibrahim Sani Shawai kuma Kafar The Fact 24 ta samu.

Kamar yadda The Fact 24 ta tabbatar, labarin da ke yawo akan wananan lamari a wata kamar Yada Labaru Karya ne kuma baya da tushe ko makama.

Wannan ya faru ne bisa ga wani lamari da ya faru a tsakanin Kamfanin da wani abokin Hulda shi, don haka wannan Labari da Kafar sadarwar ta yi karya ne.

A sabili da haka yana da kyau mutane su sani masu amfani da wutar lantarki a Katsina suna biyan abinda bai kai Kudi 10,000 a kowane wata”Cewar Takardar”.

Daga nan sai takardar ta bukaci jama’a da su Kauracewa yarda da irin wadannan labaru na Bogi da babu gaskiya ko tushe a tare da su.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker