Nan ba da dadewa ba Turkiyya da Girka za su ci gaba da tattaunawa kan takaddamarsu ta tekun Bahar Rum.
Ba da daɗewa ba Turkiyya da Girka za su iya ci gaba da tattaunawa kan ikirarin da suke yi na Tekun Bahar Rum amma shugabannin Tarayyar Turai da ke ganawa a wannan makon ba za su taimaka ba idan suka yi barazanar saka takunkumi, in ji kakakin shugaban na Turkiyya ya fada hakan a yau ranar Lahadi.
Membobin kungiyar ta NATO da makwabta sun kasance cikin takaddama mai zafi game da iyakokin su na nahiyar gabashin Bahar Rum. Rikici ya barke ne a watan da ya gabata lokacin da Turkiyya ta aike da jirgin ruwa don binciken gas da man fetur a cikin ruwan da ake takaddama a kai.