Zinatu Matar Gwamna

Zinatu Matar Gwamna 4 – Babi Na 1

A Laraba makon jiya, mun tsaya daidai inda aka ce: Al’adar Nakande ke nan, kullum idan ya je masallaci da Magariba, ba ya dawowa gida sai an kammala Isha’i kuma kullum da jikansa yake tafiya, kasancewar ya kai shekara goma a duniya. Yana son bin sunnar Manzon Allah (SAW), wanda ya ce a ummurci yara da yin Sallah idan sun kai shekara bakwai, amma idan sun kai goma, a iya dukansu, muddin suka k’i yin Sallah. To, shi wannan karantarwar ya d’auka kuma yake d’abbak’a ta ga dukkan yaran da suka taso a gidansa. Yau kuma ga ci gaba:

A zaune bisa tabarma ’yar Jibiya, Malam Nakande ne. Gefe guda kuwa, kwanonin tuwo da miya ne ke aje, ya kammala cin abincin dare ne ba da dad’ewa ba. Ya wanke hannuwansa da ruwan butar da ke gefensa na dama. Ya d’auko daushen goro ya b’alla, ya saka a baki, ya maida sauran b’allin a aljihu. Daga nan ya kishingid’a, yana sauraren sarautar Allah.

Kasancewar lokacin bazara ne ake ciki, zafi ya yi yawa, kullum a nan yake hutawa, kafin gari ya yi d’an sanyi-sanyi sannan ya koma turaka. Kamar wanda aka tsikara sai ya tashi wuf, ya shiga d’akinsa, ya d’auko akwatin rediyo. Tun daga cikin d’akin ya fara bud’e shi, yana murza mab’allin kamo tashi. Tashar BBC Landan yake k’ok’arin nema, domin takwas da rabi ta yi daidai.
Yana zama bisa tabarmar, yana kuwa samun sa’ar kamo tashar BBC d’in. Sauraren wannan tashar ya zame masa jiki. Ta nan yake samun labarun al’amuran da ke faruwa a fad’in duniya da kuma irin yadda ake fallasa asirin masu mulkin Najeriya. Idan ka d’ebe littattafan addini da yake karantawa daga lokaci zuwa lokaci, sai kuwa jaridun Hausa da yake yawan saye duk mako; amma ban da wannan sai kuwa yawan sauraren rediyo. Zimmarsa ta sanya ya koyi karatun Hausa, wanda haka ya ba shi damar iya karanta jaridun na Hausa, domin kuwa bai yi karatun boko ba a lokacin k’uruciyarsa.

Babu labarin da ya kama hankalinsa a lokacin da ya kamo tashar nan sai na yadda aka fayyace auren wata jarumar fim d’in Hausa, wai ita Zubaina. A BBC ya ji labarin yadda birnin Kano ya cika ya batse saboda rugund’umin aurenta. An ce shagalin ya yi kama da na wata d’iyar sarki. Duk da cewa Nakande bai mallaki akwatin talabijin ba balle na’urar bidiyo amma ya dad’e da jin labarin yadda ’yan wasan Hausa ke toya wainarsu, musamman a Jihohin Arewacin Najeriya.

Labarin nan da ya ji a BBC, shi ya sosa masa inda ke masa k’aik’ayi. Ba wani abu ba ne illa yadda d’iyarsa Zinatu ke zaman kashe zani a gida, alhali ta isa ko kuma a ce har ta wuce minzalin aure. Ita ba aiki ba kuma tuni ta kammala makaranta. A son ransa, babu abin da yake muradi illa ta samu miji, ya yi mata aure.
Kamar an yi sara a kan gab’a, yana cikin wannan lissafin duna sai ga Tabawa ta zo wajensa, ta duk’a kusa da shi; ta nemi izinin zuwa barkar haihuwa a mak’wafta.
“Yawwa, gwamma da kika zo yanzu; kafin ki fita zuwa barkar nan, ina da magana da ku, ke da d’iyarki, don haka ki kirawo ta nan.”

Inji Malam Nakande, yana magana yana muntsuna idanu kamar marar gaskiya. Ita kuwa daga nan ta d’aga murya kad’an, ta k’wala wa Zinatu kira. Cikin k’ank’anen lokaci Zinatu ta iso wajen iyayenta, ta durk’usa ta gaishe da babanta sannan ta samu wuri ta zauna cikin ladabi. Ta zauna nesa kad’an da shimfid’ar baban nata. Irin yadda ta takure jikinta, mutum zai gane cewa tana cikin shakka da tsoro. Babu ko shakka ta san abin da ke biyo bayan irin wannan kira na babanta, balle ma kwanan nan ya matsa mata da maganar aure. Ita kuwa abin na k’ona mata rai matuk’a, sai dai babu yadda za ta yi da abin da ya gagari wuta, wai inji kishiyar babbakakkiya.

“Tabawa, ga ki ga d’iyarki; shin yaya kuke so da ni?” Tambaya ce mai cike da k’alubale tare da alamar fushi. Yana gama fad’in haka sai ya murtuke fuska da alamar b’acin rai. Bai bari sun furta komai ba sai ya ci gaba da bayaninsa mai kama da fad’a.
“Na ga alamar kuna son mayar da ni mutumin banza a garin nan, kodayake ni ba ni ganin laifin kowa sai ke Tabawa. Ke ce ke d’aure wa d’iyarki gindi, ga shi tana neman ta gagare mu. Yau dai shekarun Zinatu talatin da biyu a duniya amma kamar wacce aka yi wa baki, ta kasa fiddo da mijin aure!”

Jin wannan kalami na babanta, Zinatu sai ta ji kamar an watsa mata garwashin wuta a jiki. Da ma ta san a rina, wai an ari zanen mahaukaciya. Tun d’azu ta ga take-taken cewa yau sai iyayenta sun yi mata kwarmato, domin kuwa ta lura da yadda Tabawa ta matsa mata da fad’a tun d’azu, balle kuma lokacin da baban nata ya dawo, ta gaishe shi amma ya amsa ciki-ciki, kamar wacce ta kashe masa d’an auta. Ta sake sunkuyar da kai, tana ci gaba da sauraren su, musamman ta zak’u ta ji amsar da innarta za ta fad’a game da wannan tambaya.
“To Malam, al’amarin Allah ai sai kallo. Kuma shin…” Tabawa ba ta ida wannan magana ba sai ya katse mata hanzari.

“Dakata, dakata. Babu ruwan Allah cikin wannan al’amari.” Yana magana yana nannaga hannunsa ga b’angarenta, da alamar cewa ta bar magana. Bai ankara ba har rediyon da ke bisa cinyarsa ya fad’o kan shimfid’arsa. Ya sanya hannu ya d’auke shi ya kulle, ya nad’e eriyarsa ya aje gefe guda sannan ya ci gaba da maganarsa mai kama da sababi.
“Ki dai gaya mani cewa ke da ita kuna da wani shiri na b’oye da ba ku sanar da ni ba. Idan ba haka ba, ’ya’ya mata nawa na aurar a gidan nan? Idan kin mance duk da cewa ke kika haife su, bari in tuna maki cewa na aurar da guda biyar kuma kowacce tana d’akin mijinta. Ki gaya mani, duk cikinsu wacce ce ta d’ara shekara ashirin a gabana ba ta yi aure ba? Sai kuwa ita Zinatu ’yar autarki, shafaffa da mai.”

Magana yake ba sassautawa. “Ke kika matsa mani lamba cewa sai ta yi karatun boko mai zurfi, ga shi ta gama karatun amma babu mijin aure.” Nisawar da ya yi kafin ya ci gaba da magana sai Tabawa ta samu damar yin magana.
“A’a Malam, ba gardama zan yi maka ba amma kowane al’amari ai na Allah ne. Ai ka fi ni sani, tun da ka karanta. Tabbas, kowane abu ka gani yana da lokacinsa. Don Allah ka k’ara hak’uri, komai mai wucewa ne!”

Wannan bayani na matarsa, maimakon ya huce masa zuciya sai ya ji wani bak’in ciki ya tokare masa k’irji. Wannan ya sanya ya rufe ido, ya ci gaba da magana. “Wane hak’uri, wane irin hak’uri zan yi da abin takaici? Bayan kun maida ni dattijon banza, na zama abin kwatance a gari. Ki duba fa, duk k’awayenta sun dad’e da tsufa a gidajen aurensu, ita kuwa sai iya karatun aku da ziyarar k’awaye. To, wallahi ba zan ci gaba da lamuntar wannan wulak’ancin ba. Ya zama dole a yi wa tufk’a hanci, a san wacce za a yi. Idan ba haka ba kuwa ni da ku!”
***
ZA A CI GABA RANAR LARABA, IN SHA ALLAH!
———————————-
© #Bashir_Yahuza_Malumfashi
Litinin 25-06-1442 (Hijriyya)
08-02-2021 (Miladiyya)
———————————-

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker