Zinatu Matar Gwamna

Zinatu Matar Gwamna 3 – Babi Na 1

A Litinin da ta gabata, mun tsaya daidai inda aka ce: Zinatu na gama wannan batu sai Balaraba ta amshe, ta ce: “Ni dai ina ganin mu bi a hankali da iyayenmu, mu lallab’a da su, mu rabu lafiya. Tun da dai mun yi karatun nan na zamani, sai mu k’ok’arta mu yi ta rok’on Allah Ya koro mana da mazajen aure. Mu yi aurenmu mu huta, alabashi idan muna d’akunan mazajenmu sai mu san hikimar da za mu shawo kansu, su bar mu mu ci gaba da neman ilimi ko kuma ma mu yi aiki ko sana’ar neman kud’i, don rufin asirin kanmu.” Da wannan zancen ne suka kawo inda za su rabu, kowace ta kama hanyar gidansu. Yau kuma ga ci gaba:

Firgigit, Zinatu ta waiga baya, mahaifiyarta Tabawa ta k’wala mata tsawa, saboda ganin da ta yi mata cikin tagumi. Wannan tsawa ce ta dawo da ita cikin hayyacinta, wanda haka ya sanya ta gane cewa, ashe tunanin k’awarta take, gani take kamar mafarki ne ta yi. Ba ta ce wa mahaifiyarta komai ba sai ta fara d’aukar kwanonin da ta wanke zuwa kicin. Bayan ta gama, ta d’auko wata guntuwar tsintsiya, wacce ta yi kama da ta share kashin yara, ta zo daf da magudanar ruwa, ta fara share ruwan wanke-wanken da ya taru.

Tana gama wannan aikin sai ta shiga d’akin mahaifiyarta, ta d’auko wani littafi na Hausa, ta zauna bisa kujera a bakin k’ofar d’akin; ta fara karantawa. A lokacin kuwa, Tabawa na can cikin kicin, tana k’ok’arin kad’a miya; jib’i kasharb’an ya rufe ta. Wani abu da ya k’ara mata wahala a kicin d’in shi ne, babu isassar taga, wacce haske da iska za su rik’a shigowa ciki; sannan kuma ga hayak’i ya turnuk’e ta. Sannan kicin d’in kuwa ya cika da kukkunniya, ya koma kamar matoya tukwane.

Tana gama burka miyar kuka, ta d’ora ruwan talgen tuwo ke nan, sai ta ji sallamar Malam Nakande, mijinta ya dawo daga wurin sana’arsa. Don haka ta fito daga kicin d’in, ta gaishe shi, shi kuwa ya amsa. Ita ma Zinatu ta d’aga kanta daga shafin littafin da take karantawa, ta gaishe da babanta. Shi kuwa ya amsa ciki-ciki, sannan ya sanya kai ya wuce turakarsa, bayan ya aje jakar ledar da ke hannunsa kusa da ita.

Zinatu ta kai wa jakar ledar nan hari da nufin ganin abin da ke ciki, ta bud’a sai ta iske lemun zak’i ne ciki. Tabawa kuwa ta ce da wa aka had’a ta, ba da ita ba?
“To, a-cici-kajin-birni! Babu abin da kika iya, daga cin abinci sai karance-karancen littattafan boko. Kin kama leda da bud’ewa, alhali Malam ko hutawa bai yi ba!” Cikin fad’a take maganar nan, ga jib’i na bi mata fuska yare-yare; sai k’arni take saboda hayak’in da ta sha a kicin.

Za ta ci gaba da sababi ke nan sai ga jikokinta biyu sun shigo gidan. Tare da sallama suka shigo, amma a guje suke, suna kokoyi da juna. Yara ne k’anana. Murtala, shekararsa goma, k’anwarsa Badiyya, shekararta takwas. Daga makarantar Islamiyya suka dawo. Shigowarsu ta d’auke hankalin Tabawa daga batun Zinatu, ta koma kan jikokin nan nata.
“Kai, kai sarakan giggiwa, ku samu wuri ku zauna; ba na son wad’annan wasannin naku na banza.” Cikin murtukakkar fuska da zare ido take masu magana, don haka suka tsorata. Suka samu wuri suka zauna kusa da Zinatu, wacce suke kira da anti.

Tabawa ta amshi ledar daga hannunta, ta d’auko wuk’a ta yayyanka lemun, ta damk’a masu. Cikin murna suka amsa, suka fara sha. Ita kuwa Zinatu ta yi zuciya, ta maida hankalinta ga karatun littafin da ke hannunta tun d’azu.
Littafin nan ne ma ya d’an huce mata takaici, domin sai ta rik’a tunani da sha’awar cewa, da ma a ce ita ce tauraruwar cikin littafin. Wato ta rik’a riyawa a zuciyarta, da ma a ce irin rayuwar Bebi Salimat take ciki. Ai kuwa da ta huce wa kanta takaici.
Irin yadda Binta Tukur ke siffanta rayuwar Bebi Salimat a cikin littafinta mai suna Son Kowa, abin ya shalle ta k’warai. Nan take sabon tunani ya kama ta, ta aje littafin gefe guda. Ba ta san lokacin da ta lula cikin iyon tunanin ba.

“Da ma dai a ce iyayena kamar irin na Bebi Salimat ne. Ga su attajirai masu kula da zamani da abin da yake ciki!” Zinatu ke sak’e-sak’en zuci, alhali ta k’ura wa Murtala da Badiyya idanu, tana kallon yadda suke tsotson lemun da Tabawa ta damk’a masu. Ta ci gaba da sak’e-sak’en zucinta.
“Bebi Salimat ta dace, an bar ta ta yi karatu mai zurfi, ga ta ’yar hutu; abinci ma sai dai a kai mata d’aki. Ba ta san wata wahala ba. Ga ta da wayar salula, ga ta kewaye da ’yan uwa da k’awaye; ga kuma kawunta mai ji da ita. Da ma ni, inji matar Mani…!”

“Anti, anti, ga naki lemun nan, ko ba ki sha?” Badiyya ce ta katse mata zaren tunanin da take ta k’ullawa, a yayin da take nuna lemun da ke kusa da ita.
“Na gani, ku d’auka ku shanye.” Inji Zinatu, cikin alamar da ke nuna cewa lemun ya fita daga ranta.
Murtala na jin haka sai ya kai wa ledar lemun hari da hannunsa, ita kuwa Badiyya da yake ta fi kusa da ledar, ta riga shi kamawa. Nan suka shiga tak’addama da juna, kowa ya kama kunne d’aya na ledar; lemu d’aya da ke cikinta ya rik’a reto.

Ganin irin yadda husuma ta shiga tsakaninsu, sai Zinatu ta amshe lemun, ta d’auki wuk’a ta raba shi biyu; ta mik’a wa kowa rabi. Shi ke nan ta raba gardamar.
A daidai wannan lokacin ne Malam Nakande ya fito da buta a hannu, ya zauna bakin k’ofar turakarsa, ya fara alwalla. Bai ida alwallar ba sai ya ji ladani ya k’wala kiran Sallar Magariba. Nan da nan ya hanzarta, ya kammala. Ya kira jikansa Murtala, ya ce masa ya yi alwalla don su tafi masallaci.

Al’adar Nakande ke nan, kullum idan ya je masallaci da Magariba, ba ya dawowa gida sai an kammala Isha’i kuma kullum da jikansa yake tafiya, kasancewar ya kai shekara goma a duniya. Yana son bin sunnar Manzon Allah (SAW), wanda ya ce a ummurci yara da yin Sallah idan sun kai shekara bakwai, amma idan sun kai goma, a iya dukansu, muddin suka k’i yin Sallah. To, shi wannan karantarwar ya d’auka kuma yake d’abbak’a ta ga dukkan yaran da suka taso a gidansa.
***
(Hoton Bango: Haqqin Mallakar #Muhammad_Bulama daga #Aminiya)
ZA A CI GABA RANAR LITININ, IN SHA ALLAH!
———————————–
© #Bashir_Yahuza_Malumfashi
Laraba 20-06-1442 (Hijriyya)
03-02-2021 (Miladiyya)
———————————–

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker