Tsaro
Yanbindiga Sun Kashe Dan Kasuwan Edo Sa’o’in Sunan Dansa

Wasu ‘yanbindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe wani dan kasuwa, Justice Abu Oshioke, a Ekpoma, Jihar Edo, sa’o’i kadan kafin bikin suna na dansa.
An ce an kai masa hari ne yayin da ya fita dauko kayan bikin. Ya rasu bayan an garzaya da shi asibiti. ‘Yan sanda sun ce an fara bincike tare da farautar wadanda suka aikata laifin..





