Tsohon Gwamnan Bauchi: A Ci Gaba da Ayyuka, Ba Bincike ba

Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Ahmad Adamu Mu’azu, ya shawarci duk wata gwamnati da za ta karbi ragamar mulki a jihar Bauchi a nan gaba da ta guji bata lokaci wajen binciken gwamnatin Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, maimakon haka ta mayar da hankali kan ci gaba da ayyukan alheri da aka gada.
Ahmad Mu’azu ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron lakca da aka shirya domin bikin cikar shekaru 50 da kafuwar Jihar Bauchi, wanda aka gudanar a dakin Taro na Ƙasa da Ƙasa na Ahmadu Bello da ke Bauchi.
Tsohon gwamnan ya jaddada cewa shi mai ra’ayin ci gaba da kyawawan ayyuka ne, yana mai cewa bata lokaci ne gwamnati ta rika shiga bincike da rigingimun siyasa, maimakon mayar da hankali kan aiwatar da manufofin da za su amfani al’umma kai tsaye.
A cewarsa, gwamnatin Bala Mohammed ta yi kokari matuka, musamman a bangaren manyan ayyukan more rayuwa da aka shimfida a sassa daban-daban na jihar, wanda ya kamata a gina a kai domin kara dorewar ci gaban Bauchi.
Ya kara da cewa abin da ya fi dacewa shi ne sabuwar gwamnati ta gina a kan tubalin da aka riga aka kafa, domin kauce wa rikice-rikicen siyasa da ka iya hana jama’a cin gajiyar dimokuradiyya.
Ahmad Mu’azu ya kuma bayyana burinsa na ganin Jihar Bauchi ta zama mafi alheri a nan gaba, inda za a samu hadin kai, zaman lafiya da goyon bayan juna a tsakanin al’ummar jihar.





