Shugaban Hikima Radio, Abubakar Isah Dandago, Ya Ajiye Aiki

Fitaccen dan jarida na kasa da kasa, gogagge a fagen rahotannin wasanni, kuma Shugaban Tashar Hikima Radio, Alhaji Abubakar Isah Dandago, ya sanar da ajiye aikinsa da gidan rediyon.
Arewa Updates ta ruwaito cewa Dandago ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya gode wa mamallakin tashar da shugabanninta bisa damar da aka ba shi na hidima.
A cikin sanarwar, tsohon shugaban tashar ya nemi afuwa daga duk wanda ya samu sabani da shi a lokacin da yake bakin aiki, yana mai bayyana cewa shi ma ya yafe wa kowa, tare da addu’ar Allah Ya gafarta wa kowa.
Dandago ya kuma jaddada cewa, ko da bayan barin aikinsa, zai ci gaba da ba da gudunmuwa da goyon baya ga duk wani ci gaba da ya shafi Hikima Radio, yana mai bayyana tashar a matsayin wani bangare na rayuwarsa.
WAYE ABUBAKAR ISAH DANDAGO?
Abubakar Isah Dandago na daga cikin manyan kwararrun ’yan jarida da Allah Ya albarkaci Jihar Kano da su. Ya shahara wajen kwarewa, jajircewa da hangen nesa a aikin jarida, musamman a fagen labaran wasanni.
Ya fara aikinsa ne a Freedom Radio Kano (Muryar Jama’a), daga nan ya koma Freedom Radio Dutse. Daga bisani ya yi aiki a tashoshin Express Radio Kano, Aminci Radio Kano da Vision FM Kano.
Ya riƙe muƙamai daban-daban a kafafen yaɗa labarai kafin daga bisani ya zama Shugaban Tashar Hikima Radio na farko. A lokacin jagorancinsa, Dandago ya taka muhimmiyar rawa wajen haɓaka tashar, inda ya yi amfani da hikima da basira wajen kai ta matsayin da take a yau.
A fagen wasanni, Dandago ya yi fice matuka. Shi ne mashahurin mai furucin “An nana wa Onana,” kuma shi ne ya jagoranci fassarar Gasar Cin Kofin kwallon kafa ta Duniya zuwa harshen Hausa. Haka kuma, shi ne wakilin Sashen Hausa na Rediyon Faransa (RFI) a Jihar Kano.
Dandago ya raini ’yan jarida da dama, wadanda a yau suke aiki a kafafen yaɗa labarai na cikin gida da na ƙasashen waje. Ya kuma bayar da gagarumar gudunmuwa wajen bunƙasa aikin jarida a Kano.
Haka zalika, shi ne Babban Jami’in Yada Labarai na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars.
Za a iya cewa Dandago ya yi dogon hidima mai cike da ƙalubale da nasarori a fagen aikin jarida, kafin daga bisani ya yanke shawarar hutawa.
Ajiye aikinsa ya girgiza zukatan ma’aikatan Hikima Radio da dama, musamman ganin cewa hakan ya zo ne kwanaki kadan bayan ajiye aiki da wani fitaccen ma’aikaci a sashen siyasa, Malam Aliyu Sufyan Alhassan.





