Labarai

Shin An Yi Garkuwa Da Dan Ministsan Sadarwa Farfesa Sheikh Isa Ali Pantami?

Almajiran Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami da ’yan sanda sun ce har yanzu ba su sa masaniya game da zargin yin garkuwa da dan ministan.
A ranar Alhamis kafofin sada zumunta suka yayata cewa an yi garkuwa da dan ministan a kusa da ginin NIDB da ke garin Bauchi.
Majiyoyi sun bayyana cewa sunan yaron Alamin Isa Ali Pantami, kuma yana zaune ne tare da mahaifiyarsa a garin Bauchi.
Aminiya ta tuntubi Babban Limamin Masallacin Juma’a na Isa Ali, wato Imam Hussaini, amma ya bayya wa wakilinmu cewa ba shi da masaniya game da sace yaron, amma zai bincika idan gaskiya ne zai sanar da mu.
Mun kuma tuntubu Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, Mohammed Ahmed Wakil, shi ma ya ce ba a kawo musu rahoton aukuwar lamarin ba.
Majiya: Aminiya

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker