Ruwanda Ta Karbi Bakuncin Taron Kasuwancin Afrika Na 16

Jamhuriyar Ruwanda na karbar bakuncin taro karo na 16 da ya hada shugabannin manya da kananan kamfanoni daga sassa daban-daban na Afrika domin tattauna hanyoyin bunkasa masana’antu da kasuwancin nahiyar.
Taron ya hada jami’an gwamnati, masu zuba jari, yan kasuwa da masana harkokin tattalin arziki, inda suke musayar ra’ayoyi kan yadda za a karfafa masana’antu na cikin gida, tallafa wa kananan kamfanoni, da samar da guraben aiki ga matasa.
Maharta taron na kuma duba matsalolin da ke hana ci gaban kasuwanci da masana’antu a wasu kasashen Afrika, tare da nemo hanyoyin hadin kai domin bunkasa tattalin arzikin nahiyar.
Shugabannin da suka halarci taron sun bayyana cewa haɗin gwiwa tsakanin kasashen Afrika da karfafa samar da kayayyaki a cikin gida zai taimaka wajen rage dogaro da kasashen waje tare da inganta ci gaba mai dorewa a nahiyar.





