Rudani a Katsina: Jami’in Kwastam Ya Rasu Bayan Kwana Da Mata Uku a Otal

Daga Zagazola Makama – Rahoto Na Musamman – An samu rasuwar wani jami’in Hukumar Kwastam mai suna Lawal Tukur, mai mukamin Assistant Superintendent of Customs (ASC), a cikin ɗakin wani otal da ke cikin garin Katsina.
Rahotanni daga Zagazola Makama sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne da safiyar Talata, 15 ga Oktoba, 2025, a Murjani Hotel, inda mamacin ya sauka tun daren jiya.
Bayanan da aka tattara sun bayyana cewa ma’aikatan otal ɗin ne suka gano gawar jami’in da misalin ƙarfe 8:30 na safe, inda suka yi kiran gaggawa ga jami’an tsaro bayan sun ga bai motsa ba tun daga safe.
Wani ganau a otal ɗin ya bayyana cewa an samu kananan kwalayen magunguna da wasu sinadarai a cikin kwandon shara a ɗakin da marigayin yake kwana, wanda ake zargin ya iya zama musabbabin mutuwa.
A yayin bincike, an gano cewa akwai mata uku da ake zargin suna da hannu ko kuma suna tare da mamacin a lokacin da lamarin ya faru.
Sun haɗa da:
- Khadija Ali, mai shekaru 34, daga unguwa Dutsin-Amare a Katsina,
- Aisha Lawal, mai shekaru 30, daga ƙaramar hukumar Ingawa,
- Hafsat Yusuf, mai shekaru 22, daga unguwa Brigade da ke Kano.
Majiyoyi sun ce Khadija da Aisha ne suka kwana tare da jami’in a daren kafin mutuwarsa, yayin da Hafsat ta iso daga baya ta tarar da su a otal ɗin.
An garzaya da gawar marigayin zuwa Federal Medical Centre (FMC) da ke Katsina, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa, kuma aka ajiye gawar a dakin ajiyar gawa domin yin binciken likitanci (autopsy).
Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta tabbatar da samun rahoton faruwar lamarin, tana mai cewa an kaddamar da cikakken bincike domin gano musabbabin mutuwar jami’in.