Wasan Kwaikwayo

Radeeya Jibril Tayi Aurenta, Ta Bar Kannywood

Tace Assalamu Alaikum, barka da safiya, ‘yan uwa da masoyana. Ina fatan kowa na cikin koshin lafiya da alkhairi a wannan sabuwar shekara.

Ni ce Radeeya Jibril, kamar yadda kuka sani, matashiyar jarumar Kannywood. Alhamdulillah, ina alfahari da kasancewata ɗaya daga cikin masu ba da gudunmawa a harkar fina-finan Hausa. Amma yau ina amfani da wannan damar don sanar da ku cewa:

“NAYI AURE!”

Alhamdulillah, Allah ya nuna min wannan rana mai albarka, ranar da zan bar Kannywood lafiya kamar yadda na shigo cikin ta lafiya. Na gode wa Allah bisa wannan ni’ima.

Ina roƙon duk wanda na taɓa yiwa kuskure ya yafe min. Ni dai ba wanda ya taɓa yi min komai ba. 🙏🏻🥺

GODIYA TA MUSAMMAN

Na keɓe wannan lokacin na gode wa wasu manya da suka taka rawa a rayuwata a masana’antar Kannywood:

1.Uncle Ty Shaba (@official_tyshaban):

Babu kalmomi da za su iya bayyana irin rawar gani da ka taka a rayuwata. Ka zama ginshiƙi, jagora, gwarzo. Allah ya saka maka da gidan Aljanna Firdausi. 🙏🏻😭

2.Abubakar Maishadda (@realabmaishadda):

Ka ɗauke ni tamkar kanwarka, ka ba ni gudunmawa, ka yi farin ciki da duk wani alkhairi da ya same ni. Allah ya saka maka da alkhairi, ya kara daukaka darajar ka. 👏👏

3.Umar UK (@reelumaruk):

Ka kasance jagora gare ni, ka ba ni shawarwari masu amfani. Allah ya saka maka da mafi kyawun alkhairi. 🙏🏻

4.AbdulaMart Mai Kwashawa (@abdulamart_mai_kwashewa):

Ka rike hannuna da niyyar ganin na samu cigaban rayuwa. Allah ya saka maka da alkhairi, ya kara haskaka maka al’amuran ka. 🙏🏻

5.Ahmad Bifa (@ahmadbifa007):

Mutum mai hakuri da halaye nagari. Nagode, Allah ya saka da alkhairi. 🙏🏻

6.Mujahid M. Soja (@real_mujahid_m.soja):

Kai mutum ne na daban, Allah ya ci gaba da daga darajar ka. 👍💯

FATANA GA KANNYWOOD

Ina yiwa dukkan al’ummar Kannywood godiya tare da fatan alkhairi. Allah ya cika wa kowa burinsa, ya sa mu yi rayuwa mai cike da nasara da albarka. ❤️💯🙏🏻

Wannan shi ne farkon sabon babi a rayuwata. Allah ya sa alkhairi ya kasance a cikin wannan sabon mataki na rayuwa. Amin.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker