PCRC da NSCDC da Hedikwatar OPHK sun ƙarfafa haɗin kai wajen yaki da matsalolin tsaro
Kwamitin Hulɗar ‘Yan Sanda da Jama’a (PCRC) tare da tawagar NSCDC sun gana da Kwamandan Rundunar Hadin Gwiwa OPHK domin ƙarfafa haɗin kai kan harkokin tsaro a Arewa maso Gabas.

By Hassan sani saidu
Kwamitin Hulɗar ‘Yan Sanda da Jama’a (PCRC), reshen jihar Borno, ƙarƙashin jagorancin Shugaba, Ambasada Abatcha Umar Nanabe, ya kai ziyara zuwa Hedikwatar Rundunar Hadin Gwiwa, Operation Hadin Kai (OPHK), domin tattaunawa kan hanyoyin haɗin kai a nan gaba don ƙara inganta tsaro a Arewa maso Gabas da Najeriya baki ɗaya.
Ambasada Nanabe ya nuna godiya ga OPHK bisa halarta da goyon baya a bikin kammala taron horo na farko kan tsaro da PCRC ta shirya a Jami’ar Maiduguri. Ya bayyana cewa irin wannan goyon baya yana ƙarfafa zumunci da haɗin kai tsakanin rundunar, hukumomin tsaro na paramilitary, da jama’a wajen kawar da ta’addanci a Borno, Arewa maso Gabas da Najeriya baki ɗaya.
A yayin ziyarar, Ambasada Nanabe ya yi ta’aziyya ga Kwamandan Rundunar kan rasuwar Kwamandan 7 Military Intelligence Brigade, Marigayi Kanal Bello Umaru, wanda ya rasu a kwanakin baya. Ya tabbatar da cewa PCRC za ta ci gaba da kasancewa tare da JTF (NE) a dukkan ayyukan haɗin kan sojoji da jama’a idan aka kira su.
A nasa jawabin, Laftanar Janar Abdulsalam Abubakar ya tarbi tawagar PCRC tare da tabbatar musu da cewa Rundunar Za ta ci gaba da haɗin kai da Kwamitin musamman wajen harkokin tsaro da kuma ayyukan haɗin kan sojoji da jama’a.
Tun kafin wannan, sabon Kwamandan Hukumar Tsaro ta Civil Defence (NSCDC), Jihar Borno, Kwamanda Mohammed Hassan Agalama, ya yi kira da a ƙarfafa dangantaka da ke tsakanin Rundunar Sojin Najeriya da NSCDC wajen yaki da ta’addanci a jihar. Ya yi wannan kiran ne a lokacin ziyarar ban girma da ya kai Hedikwatar OPHK, a ranar Alhamis, 11 ga Satumba, 2025.
Kwamanda Agalama ya tuna cewa Rundunar Sojojin Najeriya ta ba da gudummawa sosai wajen horas da jami’an NSCDC, inda kuma aka ci gaba da yin aiki tare a lokutan atisaye da ayyukan tsaro na kasa. Ya jaddada cewa jami’an NSCDC suna aiki tare da sojoji wajen tsaron muhimman kadarorin ƙasa. Ya gode wa Kwamandan Rundunar bisa goyon baya, tare da neman ƙarin haɗin kai domin ci gaban tsaron ƙasa baki ɗaya.
A martaninsa, Laftanar Janar Abubakar ya gode wa tawagar NSCDC bisa haɗin kai da suka bayar tare da tabbatar da cewa Rundunar Za ta ci gaba da ƙarfafa haɗin kai musamman wajen tsaron muhimman kadarorin ƙasa bisa ga sabuwar umarnin Shugaban Ƙasa. Ya bayyana cewa Rundunar Hadin Gwiwa (Arewa maso Gabas) ta ƙunshi jami’an tsaro daga hukumomi daban-daban, wanda hakan ne ya taimaka wajen samun nasara a yaki da rashin tsaro a yankin. Ya yaba da kwazon jami’an NSCDC a fagen gaba tare da bayyana godiya kan jajircewarsu.
Ziyarorin sun ƙare da musayar kyaututtuka da ɗaukar hotunan taron a matsayin girmamawa da alamar ƙarfafa zumunci da haɗin kai domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Arewa maso Gabas.