Na saya gidan N4 200 000 da iyayena da kudin crypto mining
A zantawar mu Hausa360 da wani matashi dake babban birnin jahar gombe yau Laraba 4 ga watan december Mai suna Yahaya Muhammad yace ya saya wa iyayen sa gidan N4,200,000 da kudin crypto mining.
Yahaya yace duk coins da ya fashe kuma ya samu kuɗi yana tarawa har sai da kuɗin yakai kimar da zai iya siyan gida sannan ya sanar da iyayen sa dasu nemo gidan da yayi musu zai saya musu da kuɗin mining.
Coins da suka fashe sun hada da Notcoin, Dogs, Fintopio da Athene yace tara kuɗin ne a cikin wata biyar kadai wato daga watan biyar zuwa oktoba acikin wannan shekara ta 2024.
Ya kara da cewa ya fara harkan Mining ne tun ana yiwa ‘Yan Pi kallon mahaukata, babu irin zagi da suka da bai sha ba akan Pi saboda shine shugaban ‘Yan Pi na layin su dan shine yake taimakawa ya samarwa yan anguwan su network da zasu ringa yin mining.
Dabarar da nayi amfani da ita shine duk lokacin da Coin ta fashe nakan sayar na ajiye kudin a asusun Dollar USDT wanda haka yake karawa kudin daraja a maimakon fadiwa saboda hakan yafi riba kuma Iyayena sunyi farin ciki sosai da ban taba gani ba cewar Yahaya Muhammad.