LabaraiSiyasa

MSF Ta Gargadi Kan Damina A Zamfara

Kungiyar likitocin agaji ta Médecins Sans Frontières (MSF) ta bayyana cewa lokacin damina na kara taazzara yawaitar cututtuka da kuma matsalar karancin abinci a jihar Zamfara, lamarin da ke jefa al’umma cikin mawuyacin yanayi.

MSF ta ce ana samun karuwar yaduwar cututtuka irin su zazzabin cizon sauro, kwalara, da kuma rashin isasshen abinci mai gina jiki, musamman a tsakanin yara kanana da mata masu juna biyu a yankunan da matsalar tsaro ta fi kamari.

Kungiyar ta kara da cewa yawan ruwan sama tare da rashin tsaftar muhalli da karancin ruwan sha mai tsafta na daga cikin manyan dalilan da ke kara bazuwar cututtukan.

Haka kuma ta bayyana cewa tabarbarewar tsaro a wasu sassan jihar na hana manoma yin noma yadda ya kamata, abin da ke kara ta’azzara matsalar karancin abinci da yunwa a yankunan da abin ya shafa.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker