Makaman Rokar Iran Sun Fada Tsakiyar Isra’ila

Wasu makaman roka da Iran ta harba sun fada a yankuna masu cunkoson jama’a a tsakiyar Isra’ila da safiyar yau Asabar.
Rahotanni sun ce ma’aikatan agajin gaggawa sun garzaya wuraren da abin ya faru a biranen Petah Tikva da Ramat Gan domin duba halin da ake ciki da kuma taimaka wa waɗanda abin ya shafa.
A halin da ake ciki, hare-haren da Iran ke kaiwa a yankin Gabas ta Tsakiya na ci gaba, inda ma’aikatar harkokin cikin gida ta Bahrain ta buƙaci jama’a su nemi mafaka bayan kararrawar gargadi ta tashi a sassa daban-daban na ƙasar.
Rahotanni sun kuma nuna cewa wani wurin sarrafa iskar gas ya kama da wuta a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa sakamakon tarkacen wasu abubuwa da suka faɗo daga sama.
Haka kuma a Kuwait, an ce wasu hare-hare sun lalata wasu muhimman cibiyoyi da suka haɗa da tashoshin samar da lantarki, cibiyoyin tace ruwan sha da kuma matatar mai.





