Majalisar koli Kan Shari’ar Musulunci Ta Sake Kiran A Cire Shugaban INEC

Majalisar koli Kan Harkokin Shari’ar Musulunci a Najeriya (SCSN) ta sake jaddada buƙatar da ta yi na a cire Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, tana mai cewa ba ta yarda zai iya gudanar da zaɓen ƙasa mai zuwa cikin adalci ba.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar, wadda Sakatare Janar dinta, Malam Nafi’u Baba Ahmad, ya sanya wa hannu. Majalisar ta bayyana cewa kiran ba shi da alaka da addini ko kabilar shugaban hukumar.
Ta ce sabon bayanin da ta fitar ƙarin haske ne kan wata sanarwa da ta fitar a ranar 28 ga Janairu, wadda ta ce an sauya ma’anarta a wasu wurare, lamarin da ya sa majalisar ta ga dacewar fitar da sabuwar takarda domin fayyace matsayarta.
“Ba batun addini muke magana ba, batun nagarta da cancanta ne. Najeriya ta gudanar da zaɓuka da dama tun daga samun ’yancin kai a 1960, kuma ba a taɓa amfani da bambancin addini wajen amincewa ko ƙin amincewa da sakamakon zaɓe ba,” in ji sanarwar.
Majalisar ta bayyana cewa daga shugaban hukumar zabe na farko a shekarar 1960, Eyo Esua, zuwa yanzu, INEC ta samu shugabanni 13, inda biyu kacal – Farfesa Attahiru Jega da Farfesa Mahmood Yakubu – suka kasance musulmai.
“Duk da haka, ba a taba samun lokacin da musulman Najeriya suka ki amincewa da sakamakon zabe saboda bambancin addini ba,” in ji majalisar.
Sanarwar ta ƙara da cewa bukatar cire shugaban INEC na yanzu ba ta da alaƙa da addininsa, sai dai tana da nasaba da wasu abubuwan da ya aikata a baya, musamman wata takarda da ya jagoranci rubutawa a shekarar 2020, wadda majalisar ta ce ta ƙunshi kalamai masu zafi da cin mutunci ga musulman Najeriya, yankin Arewa, da kuma Usman Danfodio.
Majalisar ta yi zargin cewa a cikin takardar, Farfesa Amupitan ya yi ikirarin cewa ana yi wa kiristocin Najeriya “kisan kiyashi,” tare da kokarin alaƙanta matsalolin tsaro da ake fuskanta a Arewa da jihadin Usman Danfodio na ƙarni na 19, lamarin da majalisar ta ce ba daidai ba ne kuma yunƙuri ne na tayar da zaune tsaye.
Ta kuma bayyana takaicinta kan abin da ta kira miƙa wannan takarda zuwa ƙasashen waje, lamarin da a cewarta ke nuna Najeriya a matsayin ƙasar da kiristoci ba su da ’yancin addini.
Majalisar ta kara da cewa tun bayan fitar da waccan takarda, shugaban INEC bai fito fili ya nesanta kansa daga abubuwan da ke cikinta ba. Ta jaddada cewa shugabancin hukuma mai muhimmanci kamar INEC na buƙatar mutum wanda ke nuna cikakkiyar adalci tare da nisantar duk wani alamar bambancin addini ko kabilanci.





