Ma’aikatan Sufuri a Philippines Sun Shiga Yajin Aiki Kan Tashin Farashin Mai

Ma’aikatan sufuri a kasar Philippines sun fara wani yajin aikin kwanaki biyu a sassa daban-daban na kasar domin nuna rashin amincewarsu da tashin gwauron zabi na farashin man fetur. Wannan tashin farashin mai na da alaƙa da rikice-rikicen da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda ya janyo hauhawar farashin makamashi a kasuwannin duniya.
Direbobin motocin haya da sauran ma’aikatan sufuri sun gudanar da zanga-zanga a wasu manyan biranen ƙasar, inda suka bukaci gwamnatin Philippines ta dauki matakan gaggawa domin rage farashin man fetur. Haka kuma sun nemi gwamnati ta janye wasu haraji da ake ɗora wa man fetur da iskar gas, domin rage musu nauyin da suke fuskanta a rayuwarsu ta yau da kullum.
Masu zanga-zangar sun bayyana cewa tashin farashin mai ya matuƙar shafi harkokin kasuwanci da rayuwar su, musamman ma direbobin motocin haya da ke dogaro da mai wajen gudanar da aikinsu. Sun ce idan gwamnati ba ta dauki mataki ba, lamarin na iya jefa su cikin mawuyacin hali.
A wani bangare kuma, gwamnatin Philippines ta sanar da wasu tsare-tsare na rage radadin halin da jama’a ke ciki. Daga cikin matakan da ta dauka akwai samar da motocin jigilar jama’a kyauta a wasu yankuna domin taimaka wa al’umma su samu sauƙin zirga-zirga.
Sai dai duk da haka, masu zanga-zangar sun ce wadannan matakai ba su wadatar ba, kuma ba za su magance matsalar tashin farashin mai da suke fuskanta ba.
Rahotanni sun kuma nuna cewa a ranar Talata gwamnatin Philippines ta ayyana dokar ta-ɓaci kan makamashi a ƙasar, domin bai wa hukumomi damar daukar matakan gaggawa wajen shawo kan matsalar hauhawar farashin mai da kuma kare tattalin arzikin ƙasar.




