Labarai

IGP Ya Nada Anthony Placid a Matsayin Sabon Kakakin Rundunar Yan Sandan Najeriya

Sufeto Janar na Rundunar Yan Sandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu, ya amince da nadin Anthony Okon Placid a matsayin sabon Kakakin Rundunar Yan Sandan Najeriya ( FPRO)

Placid ya maye gurbin Benjamin Hundeyin, wanda aka sauya masa wurin aiki a wani sabon tsarin sauye-sauyen aiki da rundunar ta yi.

Gogaggen Jami’in Yan Sanda

DCP Anthony Placid gogaggen jami’i ne a cikin hukumar yansanda, wanda ya shafe shekaru yana aiki a fannoni daban-daban da suka hada da gudanarwa, ayyukan tsaro, tattara bayanan sirri, horaswa da kuma ayyukan wanzar da zaman lafiya na kasa da kasa.

An haifi Placid a ranar 2 ga Disamba, 1970 a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom. Asalinsa daga Mbiokporo Nsit a karamar hukumar Nsit Ibom.

Ilimi da Horaswa

Sabon kakakin rundunar ya samu digiri na farko (BSc) a fannin Geography da Regional Planning daga jami,ar Uyo.

Haka kuma yana da digirin digirgir (MA) a fannin Law and Diplomacy daga jami,ar Jos.

Bugu da kari, ya yi karatun Lauya (LLB) a National Open University of Nigeria.

An dauke shi aiki a rundunar yan sanda a shekarar 1996 a matsayin Cadet Assistant Superintendent of Police a Nigeria Police Academy Kano, inda aka ba shi cikakken mukami a watan Agustan 1998.

Kwarewa a Ayyukan Tsaro Na Cikin Gida Da Na Duniya

DCP Placid ya halarci darussa da horo na kasa da kasa da dama, ciki har da na United Nations Peace Operations Specialised Training (POST).

Har ila yau ya samu horo a fannoni kamar

Nazarin yan sanda (Police Studies)

Nazarin soja (Military Studies)

Kare hakkin bil’adama

Dokokin yaki na duniya (International Humanitarian Law)

Kare fararen hula a lokacin rikici

Haka kuma ya halarci UNITAR Senior Leadership and Peace building Course a kasar Kenya.

Mukaman Da Ya Rike

A tsawon aikinsa, Placid ya rike mukamai da dama a ciki da wajen Najeriya, ciki har da

Kakakin Yan Sanda (PPRO) na Jihar Adamawa

Kakakin Police Staff College, Jos

Babban jami’in horaswa a African Union Mission a Sudan

Shugaban horaswa da ci gaba a United Nations Mission a Darfur

DPO a wurare da dama ciki har da Calabar, Bakassi, Uruan da Gembu

Shugaban sashen Anti Robbery a Kaduna

Mai ba African Union shawara kan tsaron zabe

Assistant Commissioner of Police (Operations) a Akwa Ibom da Kogi

ACP mai kula da sashen bayanan sirri a Abia State

Cikakken Jami’i Mai Takardar Shaida

Placid mamba ne na International Association of Chiefs of Police, sannan kuma malami ne kan hakkin bil’adama na kungiyar Commonwealth da kuma mai horaswa a kan dokokin yaki na International Committee of the Red Cross.

Shi ma dalibi ne da ya kammala Senior Executive Course 47 a National Institute for Policy and Strategic Studies, inda aka ba shi lambar girmamawa ta Member of the National Institute (mni) a ranar 13 Disamba 2025.

Rayuwa Ta Kai Tsaye

DCP Anthony Placid mutum ne mai aure da ’ya’ya. A lokutan hutunsa yana sha’awar sauraron kida mai kyau, wasan kwallon ƙafa, kwallon kwando, tebur tennis da badminton, tare da mu’amala da jama’a.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker