IGP Disu ya dauki matakan dakile cin zarafi

Olatunji Disu, Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya, ya kaddamar da wasu muhimman gyare-gyare a rundunar domin karfafa gaskiya da rikon amana, tare da magance matsalolin cin zarafi da suka dade suna addabar jama’a.
Tun bayan hawansa mulki a ranar 24 ga Fabrairu, 2026, Disu ya mayar da hankali kan sake fasalin hanyoyin sa ido na cikin gida, ciki har da Complaint Response Unit da kuma Independent X-Squad, domin binciken laifukan da jami’ai ke aikatawa.
Sabbin matakan sun kuma dora alhaki kai tsaye a kan Kwamishinonin ‘Yan Sanda kan duk wani abu da jami’an da ke karkashinsu suka aikata.
Haka kuma, rundunar ta fara daukar matakai domin magance jinkiri da rashin tsari wajen gudanar da shari’o’in laifuka, tare da sake jaddada haramcin kafa shingayen bincike ba tare da izini ba, wanda ke da nasaba da zargin karbar kudin goro.
An kuma fitar da sabbin ka’idoji domin hana manyan jami’ai tsoma baki a bincike, domin tabbatar da cewa ana tafiyar da shari’o’i bisa ka’ida ba tare da tasiri ba.
A bangaren ma’aikata, rundunar ta yi karin girma ga sama da jami’ai 33,000, tare da ci gaba da tattaunawa kan jin dadin su, ciki har da batun gidaje da fansho.
Disu ya kuma yi wasu muhimman nade-nade, inda a ranar 8 ga Maris, 2026 aka nada DCP Anthony Okon Placid a matsayin kakakin rundunar.
Haka kuma, a ranar 12 ga Maris, 2026, rundunar ta gudanar da bikin bankwana ga tsohon Sufeto Janar, Kayode Egbetokun, wanda ya bambanta da yadda ake sauyin shugabanci a baya.
Wadannan gyare-gyare na daga cikin kokarin da rundunar ke yi domin inganta aiki, karfafa ladabtarwa, da dawo da amincewar jama’a.





