Labarai

Gwamnatin Habasha Na Shirin Tura Sojoji Zuwa Arewacin Kasar

Rahotanni daga Habasha sun nuna cewa gwamnatin kasar na tattara sojoji daga yankunan da ke fama da rikici na Amhara da Oromia domin tura su zuwa arewacin kasar, musamman yankin Tigray da kuma kan iyakar Afar.

Wata jam’iyyar adawa a yankin Amhara ta yi zargin cewa gwamnatin na janye sojojinta daga yankin, tare da yin gargaɗin cewa hakan na iya haifar da gibi a harkar tsaro idan kungiyar FANO ta yi yunkurin kwace wasu garuruwa.

A gefe guda kuma, kungiyar Tigray People’s Liberation Front (TPLF) ta zargi gwamnatin tarayya da shirin sake tayar da wani sabon rikici a yankin Tigray.

A wata sanarwa da ta fitar ranar 9 ga Fabrairu 2026, TPLF ta bukaci kasashen duniya da su matsa wa gwamnatin Habasha lamba domin dakatar da duk wani shirin soja da ka iya haddasa sake barkewar rikici a yankin.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker