
Hukumar Kula da Sha’anin Masallacin Harami da Masallacin Annabi ta bayyana cewa adadin masu ibada da masu ziyara da suka kai ziyara Masallatan Harami guda biyu a cikin watan Safar 1447 ya kai mutum 52,823,962.
Hukumar ta fitar da wannan sanarwa ne a ranar Asabar, inda ta bayyana cewa wannan adadi ya haɗa da masu zuwa yin ibada, masu ziyartar Makka da Madina, da kuma maziyartan da suka yi umrah a cikin watan.
Ma’aikatar Hajji da Umrah ta jaddada cewa wannan nasara ta nuna yadda ake samun sauƙi da tsari wajen kula da al’umma masu zuwa Masallatan Harami, tare da samar musu da tsaro, kiwon lafiya, da duk wasu abubuwan bukata.
Hukumar ta ce za ta ci gaba da ƙoƙari domin inganta ayyuka da kuma sauƙaƙa wa maziyarta damar yin ibada cikin kwanciyar hankali da natsuwa.