Ilimi
Dan jihar Borno da Yar Zamfara sun lashe Musabakar Al-Qur’ani da kyautar N6,000,000
Dan jihar Borno ya lashe gasar izu 60 ta karatun Al Kur’ani mai tsarki ta ƙasa Najeriya da aka kammala a jihar Bauchi.
Baba Sanyinna Goni Mukatar ya karɓi kyautar naira miliyan uku N3,000,000
Yar jihar Zamfara Haulatu Aminu Ishaq ce ta lashe gasar izu 60 ɓangaren mata. Ita ma ta lashe kyautar naira miliyan uku N3,000,000.
Wannan ne karo na 36 da ake gudanar da gasar da Jami’ar Usman Danfodio da ke Sokoto ke jagoranta.