Labarai

Da dumi dumin sa: Alkalin Kotu ya yanke wa Sheikh Abduljabbar hukuncin kisa ta hanyar rataya

Labarai daga shafin BBC Hausa na cewa ” Babbar kotun shari’ar Musulunci ta jihar Kano ta yanke wa Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samun sa da laifi yin kalaman rashin tarbiyya ga Annabi Muhammad.

An yanke hukuncin ne a ranar Alhamis bayan da Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya ce an same da dukkan laifukan da ake tuhumarsa da su.

Daga cikin tuhumar da ake masa, hadda zargin wa’azinsa zai iya tayar da tarzoma a jihar Kano.

Bayan an same shi da laifukan, sai Mai Shari’a Sarki Yola ya dage zaman kotun don ba shi damar rubuta hukuncin da za a yanke wa malamin.

Bayan dan lokaci kuma sai aka koma zaman kotun tare da yanke hukuncin.

Sai dai kafin a tafi hutun Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara ya yi magana ta karshe inda ya ce lauyan da ke kareshi bai san shi ba kuma baya neman afuwa saboda a cewarsa bai aikata laifi ba, don haka a gaggauta yanke masa hukunci.

A ranar Juma’a 16 ga watan Yulin 2021 ne gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da malamin a gaban kotu bisa zargin ɓatanci ga addini da kuma tunzura jama’a, zargin da ya sha musantawa.”

Da zarar mun samu wani kari bayani zamu sanar daku.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker