APC ta tsawaita sayar da fom din takara zuwa Litinin

All Progressives Congress (APC) ta sanar da tsawaita lokacin sayar da fom din takara da bayyana niyya daga ranar Asabar, 2 ga Mayu, 2026 zuwa daren Litinin, 4 ga Mayu, 2026.
Jam’iyyar ta kuma matsar da ranar mika fom daga Asabar zuwa Talata, 5 ga Mayu, 2026, yayin da za a gudanar da tantance ‘yan takara a ranar Laraba, 6 ga Mayu, 2026.
Mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyyar, Duro Meseko, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a sakatariyar APC ta kasa a Abuja.
Ya ce an dauki matakin ne sakamakon hutun gwamnati da za a yi ranar Juma’a, domin bai wa masu neman takara damar sayen fom dinsu.
A cewarsa, kwamitin gudanarwa na jam’iyyar (NWC) ne ya amince da sauyin, bayan korafe-korafe da aka samu daga jihohi daban-daban.
Meseko ya kara da cewa matakin zai bai wa dukkan masu sha’awar takara damar shiga cikin tsarin ba tare da wata matsala ba.





