Tsaro

Ana samun ci gaba a yaki da rashin tsaro a Sokoto – Ahmed Aliyu

Gwamnan jihar Sokoto State, Ahmed Aliyu, ya ce ana samun nasara a ƙoƙarin da ake yi na magance matsalar tsaro a jihar sakamakon sabbin matakan da gwamnati ta ɗauka.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin buɗe taron majalisar zartarwar jihar, inda ya ce sabon tsarin da aka fara yana haifar da gagarumar ci gaba wajen yaƙi da ayyukan ƴan fashin daji a ƙananan hukumomi 13.

Ya kuma ƙara da cewa ana samun ci gaba a yaƙin da ake yi da sauran masu aikata laifuka a faɗin jihar.

Jihar Sokoto na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da matsalar ƴan bindiga, duk da iƙirarin da gwamnatoci ke yi na samun nasara.

Sai dai har yanzu ana fuskantar hare-hare a wasu yankuna, inda ƴan bindiga ke kai farmaki kan ƙauyuka a jihar da ma wasu jihohin da ke maƙwabtaka.

Gwamna Ahmed Aliyu ya jaddada cewa gwamnati na ƙoƙari wajen dawo da zaman lafiya, ciki har da shirin mayar da waɗanda suka tsere daga gidajensu zuwa muhallansu na asali.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker