An kashe jami’an FRSC fiye da 100 a shekarar 2025 – Shugaban Hukumar

Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) ta bayyana cewa an kashe jami’anta fiye da 100 yayin da suke bakin aiki a shekarar 2025 da ta gabata.
Hukumar ta ce karuwa a yawan mutuwar jami’anta ne ya sa ta fara kira ga gwamnatin tarayya da ta ba ta damar bai wa jami’anta makamai, domin kare kansu da kuma ƙara musu kwarin gwiwa yayin gudanar da aikinsu a kan manyan hanyoyi.
Shugaban FRSC, Shehu Mohammed, ya shaida wa BBC cewa mafi yawan mutuwar jami’an na faruwa ne sakamakon direbobi da ke bugunsu yayin da suke kan aiki.
“A shekarar da ta wuce, mun rasa jami’anmu kusan 127, kuma kusan dukkansu direbobi ne suka buge su suna bakin aiki. Wannan lamari na damunmu matuƙa,” in ji shi.
Ya bayyana cewa abin da ya fi tayar da hankalin hukumar shi ne yadda ake bugun jami’an har lokacin da suke tsaye a gefen hanya.
“Abin takaici ne matuƙa direba ya buge jami’inmu alhali yana tsaye a gefen hanya. Wasu lokutan ma abin yana kama da an yi shi ne da gangan. Wannan ne ya sa muke ci gaba da faɗakar da direbobi su guji shan giya ko duk wani abu mai sa maye kafin tuƙi,” in ji shugaban hukumar.
Shehu Mohammed ya kara da cewa bai wa jami’an FRSC damar rike makami na iya taimakawa wajen rage irin waɗannan hare-hare da haɗurra.
“Shi ya sa muke kira da a ba jami’anmu damar riƙe makami. Wannan zai ƙara musu kwarjini da ƙarfin gwiwa, tare da sa direbobi su yi taka-tsantsan wajen mu’amala da su,” in ji shi.
Sai dai shugaban hukumar ya jaddada cewa idan aka amince da batun riƙe makami, to horo mai tsauri ne zai zama abin da za a ba fifiko.
“Idan aka ba mu damar rike makami, horo ne zai zama na farko. Horo zai tabbatar da bin doka, kare hakkin dan Adam, da kuma hana amfani da makami ta hanyar da ba ta dace ba,” in ji shi.





