Duniya

Amurka ta umarci babban hafsan sojin kasanta ya yi murabus

Sakataren harkokin wajen Amurka, pete Hegseth ya umarci babban hafsan sojin kasa na kasar, Janar Randy George ya sauka daga muƙaminsa, kamar yadda kafar yada labarai ta CBS kawar huldar BBC a Amurka ta ruwaito.

Kakakin ma’aikatar tsaron kasar, ta Pentagon Sean Parnell ya bayyana cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafin sada zumunta cewa ”zai sauka daga matsayinnsa na babban hafsan sojin kasan Amurka na 41 ba tare da bata lokaci ba”.

Kawo yanzu babu cikakken bayani kan dalilin da ya sa ake ce ya sauka daga mukamin nasa ba.

Matakin na na zuwa ne bayan da Shugaba Trump ya bayyana a wani jawabin da ya yi wa kasar cewa ana sa ran yakin Amurka da Isra’ila da kuma Iran a gefe guda ya kusa zuwa karshe ”nan ba da jimawa ba”.

A ka’ida babban hafsan sojin kasan Amurka kan yi wa’adin shekara hudu.

Toshon shugaban Amurka, Joe Biden ne ya nada George mukamin a 2023.

Janar George ya fara ya fara aiki da rundunar sojin Amurka ne bayan kammala karatu a makarantar horon manyan hafsoshin sojin kasar da ke West Point.

Ya halarci yakin yankin Gulf na farko a matsayin kwamandan dakarun kasa, sannan a baya-bayan nan ya halraci yake-yaken Afghanistan da Iraki.

Kafofin yada labaran Amurka sun ce za a maye gurbinsa da mataimakinsa Janar Christopher LaNeve a matsayin riko.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker