Siyasa

ADC Kano: Masu Neman Takara Sun Barranta Daga Takardar Tuhuma

Wasu masu neman takarar ADC a Kano sun barranta kansu daga takardar tuhumar da aka shigar. Sun ce ba su bai wa izini ba.

Wasu masu neman takarar Majalisar Wakilai da Majalisar Dokokin Jihar Kano a Jam’iyyar ADC sun barranta kansu daga takardar tuhumar da aka aika wa Kwamared Muhammad Tukur Warawa. Takardar ta zargi Hajiya Naja’atu Muhammad da karbar kudi domin ba masu neman takara damar tsayawa takara.

Shugaban ƙungiyar ADC Kano State Support Group, Hon. Muhammad Yusuf Babba Dan Agundi, ne ya sanya wa hannu a ranar Laraba 24 ga Yunin 2026. Takardar ta ce wasu daga cikin masu neman takara 44 da aka ambata sun ce ba su bai wa Hon. Sa’idu Nakowa izinin wakiltarsu ba.

Ƙungiyar ta bukaci Barrista Mubarak Muhammad na Definite Edge Consultants da ya cire sunayen wadanda abin ya shafa. Ta ce za su dauki matakin shari’a idan ba a cire sunayensu cikin sa’o’i 24 ba.

Wannan na kara fito da tsamin dangantakar da ke tsakanin ɓangaren Hajiya Naja’atu Mohammed da tsagin Hon. Musa Ungogo. Wannan dai tsohuwa da sabuwar ADC ce a Kano.

Rikicin na ADC Kano na kara tsananta yayin da ake shirin zaɓen 2027. Bangarorin biyu suna fafutukar neman goyon baya. Sai a ga ko za a samu sulhu tsakaninsu.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

  • YAHAYA SHUAIBU

    Popularly known as Yahmis Yahaya a Media Technology Professional and Journalist with extensive experience in digital media, broadcasting technology, streaming services, and online publishing. He specializes in leveraging technology to enhance news production, content distribution, and audience engagement. As the Founder of Hausa360 Media and a media technology practitioner, he is passionate about digital journalism, technology reporting, media innovation, and the use of emerging technologies to strengthen information access and public communication.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker