AddiniWasan Kwaikwayo

Jaruma Radiya Jibril Ta Sake Aure

An daura auren fitacciyar jarumar Kannywood Radiya Jibril karo na uku, lamarin da ya jawo martani daga masoyanta.

Fitacciyar jarumar masana’antar Kannywood, Radiya Jibril, ta sake shiga gidan aure karo na uku. Jarumar ta bayyana farin cikinta da godiyarta ga Allah bayan daura auren nata, tana mai bayyana cewa aure wata kaddara ce daga Ubangiji, ta sanar da hakan ne ranar lahadi 31 ga watan mayu 2026.

A sakon da ta wallafa, Radiya Jibril ta bayyana cewa ta dade tana fatan samun zaman aure na gari. Ta ce duk wata jarabawa da ta fuskanta a rayuwar aurenta tana kallonta a matsayin kaddarar Allah.

Jarumar ta kuma yi addu’ar Allah Ya ba ta ikon kare mutuncinta da zaman lafiyarta a gidan auren da aka daura mata.

Ta roki Allah Ya sanya wannan aure ya kasance alheri gare ta, iyalanta, da makomarta. Radiya Jibril na daga cikin fitattun jaruman Kannywood da suka yi suna a fina-finan Hausa tsawon shekaru.

A baya, jarumar ta taba sanar da aurenta tare da bayyana cewa za ta rage ko ta daina harkar fim domin mayar da hankali kan rayuwar aurenta.

Sai dai bayan wasu watanni, an sake ganinta a wasu ayyukan talla da kuma harkokin fina-finai, lamarin da ya nuna cewa auren nata na baya ya kawo karshe.

Bayan rabuwarta da auren da ya gabata, Radiya ta dawo harkar fina-finai inda ta fito a wasu fitattun shirye-shirye da fina-finan Hausa.

Daga cikin ayyukan da ta sake bayyana a cikinsu akwai fim din Wani Dare da wasu tallace-tallacen kamfanoni daban-daban. Masoya Kannywood sun ci gaba da bibiyar rayuwarta da kuma ci gaban aikinta a masana’antar.

Masoya da abokan sana’ar jarumar sun taya ta murna tare da yi mata fatan samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a sabon gidan aurenta. Wasu daga cikin mabiyanta sun yi addu’ar Allah Ya sanya wannan aure ya zama mafi alheri a rayuwarta.

Daura auren Radiya Jibril karo na uku ya sake jawo hankalin masoya Kannywood. Yayin da ake taya ta murna, da dama suna fatan Allah Ya ba ta zaman lafiya, hakuri, juriya, da albarkar zuri’a a sabon gidan aurenta.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

  • YAHAYA SHUAIBU

    Popularly known as Yahmis Yahaya a Media Technology Professional and Journalist with extensive experience in digital media, broadcasting technology, streaming services, and online publishing. He specializes in leveraging technology to enhance news production, content distribution, and audience engagement. As the Founder of Hausa360 Media and a media technology practitioner, he is passionate about digital journalism, technology reporting, media innovation, and the use of emerging technologies to strengthen information access and public communication.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker