Labarai

EFCC Ta Gurfanar da Blessing CEO a Gaban Kotu

Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa ta gurfanar da fitacciyar mai amfani da kafafen sada zumunta, Okoro Blessing Nkiruka wadda aka fi sani da Blessing CEO, a gaban babbar kotun tarayya da ke Ikoyi a jihar Legas kan zargin damfara da ta kai naira miliyan 36.

An gurfanar da Blessing CEO ne bisa tuhume-tuhume guda biyu da suka haɗa da zargin yin ƙaryar rashin lafiya domin karɓar kuɗi da kuma satar kuɗaɗe.

A yayin fara sauraron ƙarar, lauyanta P.I. Nwafor ya shaida wa kotu cewa wadda yake karewa ta mayar wa mai ƙorafi kuɗinsa.

Sai dai Blessing CEO ta musanta aikata laifukan da ake tuhumarta da su.

Lauyan nata ya kuma bayyana cewa suna kokarin cika sharudan neman beli, inda ya roƙi kotu da ta amince a ci gaba da tsare ta a hannun EFCC har zuwa lokacin da za a kammala shirye-shiryen beli.

Mai shari’a Dipeolu ya amince da buƙatar tare da bayar da umarnin ci gaba da tsare Blessing CEO a hannun hukumar EFCC.

Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 5 ga watan Yuni domin ci gaba da shari’ar.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker