Farashin Mai Ya Tashi Saboda Rufe Hormuz

Farashin danyen mai ya samu karin dala uku kan kowace ganga a yau Litinin, sakamakon sabon yanayin da ya kara dagula kasuwannin makamashi a duniya.
Wannan hauhawar farashi ta biyo bayan rahotanni da ke nuna cewa Mashigin ruwan Hormuz, wanda ke da matukar muhimmanci wajen jigilar mai, ya ci gaba da kasancewa a rufe a cikin yanayin takaddama.
Rufe wannan mashigi ya kara tayar da hankalin masu kasuwanci da kasashen da ke dogaro da shigo da mai, kasancewar ana daukar shi a matsayin daya daga cikin manyan hanyoyin jigilar danyen mai a duniya.
Wannan yanayi ya janyo karancin tabbaci a kasuwannin makamashi, wanda ya sa farashin mai ya fara hauhawa cikin gaggawa.
Karanta: Iran ta gargadi Amurka kan shingen ruwan hormuz
Masana harkokin tattalin arziki sun bayyana cewa duk wani rikici ko rashin kwanciyar hankali a yankin Mashigin ruwan Hormuz na iya yin tasiri kai tsaye ga farashin mai a kasuwannin duniya.
Sun ce idan har rufewar ta ci gaba, akwai yiwuwar ƙarin tashin farashi a cikin kwanaki masu zuwa.
A halin yanzu, kasuwannin duniya na ci gaba da sa ido kan yadda lamarin zai kaya, yayin da masu ruwa da tsaki ke neman hanyoyin warware takaddamar domin dawo da jigilar mai yadda ya kamata da daidaita farashin makamashi a duniya.





