Bianca ta gode wa Tinubu kan nadinta a matsayin Minista

Bianca Odumegwu-Ojukwu, Ministan Harkokin Wajen Najeriya, ta bayyana godiyarta ga Bola Ahmed Tinubu bisa nada ta a matsayin cikakkiyar minista a ma’aikatar.
Kafin wannan nadin, Odumegwu-Ojukwu ta kasance Karamin Ministan Harkokin Waje tun ranar 4 ga Nuwamba, 2024.
A wata sanarwa da mai taimaka mata kan harkokin sadarwa, Dakta Magnus Eze, ya fitar, ya ce ministar ta bayyana hakan ne yayin wani liyafar dare da ma’aikatar ta shirya bayan kammala horo na kwanaki uku ga jakadu da manyan wakilan diflomasiyya da za a tura kasashen waje.
A jawabinta na farko a matsayin cikakkiyar minista, ta gode wa shugaban kasa bisa amincewa da ita, tare da kira ga jakadu, ma’aikata da shugabannin ma’aikatar da su hada kai domin inganta martabar Najeriya a idon duniya da kuma kare muradun kasa.
A wani sako da ta wallafa a shafinta na X, ta ce tana matukar jin dadin an karramata da wannan mukami, tare da alkawarin ci gaba da aiki tukuru domin cimma manufofin harkokin waje na gwamnatin “Renewed Hope”.
Ta kuma jaddada kudurinta na kare muradun Najeriya a duniya da kuma karfafa dangantakar kasa da kasa ta hanyar diplomasiyya mai inganci.





