Tsaro
Al’ummar Ariko sun musanta ikirarin Sojin Najeriya kan ceto masu ibada

Al’ummar garin Ariko da ke karamar hukumar Kachia a jihar Kaduna State sun musanta rahoton Nigerian Army da ke cewa dakarunta sun ceto masu ibada 31 da ƴanbindiga suka yi garkuwa da su.
An sace mutanen ne a lokacin da suke tsaka da ibada a wasu majami’u biyu a garin Ariko ranar Lahadi da ta gabata.
Rahotannin kafafen yada labarai a Najeriya sun ambato rundunar sojin kasar tana cewa dakarunta sun yi gumurzu da ƴanbindiga a cikin daji, inda daga bisani suka ceto mutanen sa’o’i kaɗan bayan an sace su.
Sai dai shugaban ƙungiyar al’ummar Kuturmi, Dakta David Joseph Ariko, ya musanta wannan iƙirari a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.





