Siyasa

Gwamnan Zamfara Dauda Lawal ya fice daga PDP, ya koma APC

Gwamnan jihar Zamfara State, Dauda Lawal, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), tare da komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a matakin tarayya.

Sanarwar hakan ta fito ne ta bakin mai magana da yawun gwamnan, Nuhu Salihu Anka, inda ya bayyana cewa gwamnan ya yanke wannan shawara ne bayan shawarwari da tuntuba da manyan masu ruwa da tsaki da kuma magoya bayansa.

A cewar gwamnan, daya daga cikin manyan dalilan da suka sa ya sauya sheka shi ne rikicin cikin gida da ya addabi jam’iyyar PDP a matakin kasa da na jiha.

Ya kara da cewa wannan rikici na haifar da rudani da kuma kawo cikas ga gudanar da ayyukan gwamnati a jihar, lamarin da ya sa ya ga dacewar ɗaukar sabon mataki domin ci gaban Zamfara da al’ummarta.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker