Tinubu Ya Nada Tunji Disu a Matsayin Sufeta-Janar Na Yan’Sanda

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da nadin Olatunji Rilwan Disu a matsayin mai rikon mukamin Sufeta-Janar na Yansandan Najeriya, bayan tsohon mai rike da mukamin, Kayode Egbetokun, ya ajiye aikinsa.
A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar, Tinubu ya ce ya amince da murabus ɗin Egbetokun ne bayan ya miƙa takardar ajiye aiki bisa dalilai na iyali.
Shugaban ya gode wa tsohon sufeta-janar ɗin, tare da yabawa gudunmawar da ya bayar cikin shekaru da dama da ya shafe yana hidimtawa rundunar ƴansanda da kuma ƙasa baki ɗaya.
A watan Yunin 2023 ne Tinubu ya naɗa Egbetokun a matsayin Sufeta-Janar na ƴansanda, inda ake sa ran zai yi wa’adin shekaru huɗu har zuwa Yunin 2027.
Sanarwar ta ƙara da cewa, bisa la’akari da ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta da kuma tanadin dokoki, shugaban ƙasa ya amince da naɗa Mataimakin Sufeta-Janar (AIG) Tunji Disu a matsayin mai riƙon muƙamin, wanda zai fara aiki nan take.
Haka kuma, kamar yadda dokar ƴansanda ta shekarar 2020 ta tanada, shugaban zai kira taron Majalisar Ƴansanda ta Ƙasa domin duba da kuma tabbatar da naɗin AIG Disu kafin a miƙa sunansa ga Majalisar Dattawa don amincewa.
Wane ne Tunji Disu?
An haifi Olatunji Rilwan Disu a jihar Legas ranar 13 ga Afrilu, 1966.
Ya shiga aikin ɗansanda a ranar 18 ga Mayu, 1992, kuma ana sa ran zai yi ritaya a shekarar 2026.
Disu ya taɓa jagorantar Sashen Kai Ɗauki da Tattara Bayanai na rundunar ƴansandan Najeriya bayan sauke Abba Kyari. Haka kuma ya riƙe muƙamin kwamandan Rundunar Kai Ɗaukin Gaggawa ta jihar Legas.
Ya kuma yi aiki a matsayin Mataimakin Kwamishinan Ƴansanda a sashen gudanar da ayyuka a shalkwatar rundunar da ke Abuja, sannan ya taɓa zama mataimakin shugaban sashen binciken manyan laifuka a jihar Rivers.
Bugu da ƙari, ya jagoranci tawagar ƴansandan Najeriya da aka tura Darfur, a ƙasar Sudan, ƙarƙashin shirin tabbatar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya.
A ɓangaren ilimi, Disu ya yi digiri na farko a fannin Turanci a Jami’ar Jihar Legas (LASU), sannan ya yi digiri na biyu a fannin gudanar da mulki a Jami’ar Adekunle Ajasin da ke jihar Ondo.
Ya halarci kwasa-kwasai da dama a cikin gida da ƙasashen waje, ciki har da horo kan yaƙi da safarar ƙananan makamai a Botswana, horo kan zamba ta intanet a Jami’ar Cambridge da ke Birtaniya, da kuma kwasa-kwasai kan dabarun shugabanci da binciken manyan laifuka a Najeriya.





