OIC Ta Yi Allah-wadai da Harin Zamfara, Ta Nemi A Sako Wadanda Aka Sace

Kungiyar Kasashen Musulmai ta Duniya (OIC) ta bayyana matukar damuwarta kan harin da aka kai a jihar Zamfara a ranar 21 ga Fabrairu, 2026, wanda ya yi sanadiyyar kashe fararen hula tare da sace mata da yara.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta soki harin da kakkausar murya, tana mai cewa irin wannan aiki ya saba wa ka’idojin dan adam da kuma koyarwar addini.
Kungiyar ta jajanta wa gwamnatin Najeriya da al’ummar kasar bisa wannan mummunan lamari, tare da mika ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, da kuma yi wa waɗanda suka jikkata addu’ar samun waraka cikin gaggawa.
Haka kuma, OIC ta yi kira da a gaggauta sakin mata da yaran da aka yi garkuwa da su ba tare da wani sharadi ba, domin su koma ga iyalansu cikin koshin lafiya.
Kungiyar ta kara da jaddada aniyarta na ci gaba da goyon bayan kasashe mambobinta wajen yaki da ta’addanci da duk wani nau’in rashin tsaro.





