Kasuwanci

Sabuwar gobara ta sake tashi a Kasuwar Singa ta Kano

Wata sabuwar gobara ta sake barkewa a Kasuwar Singer da ke Kano, inda ta lalata shaguna da dama a bangaren Gidan Glass na kasuwar da ke kan titin Ado Bayero kusa da Murtala Muhammad Way.

Lamarin, wanda ya fara ne da yammacin ranar Asabar, shi ne gobara ta biyu da ta auku a kasuwar cikin kasa da makonni biyu.

Wani dan kasuwa, Nasir Maharazu, ya shaida wa Hausa360 cewa gobarar ta fara ne da misalin karfe 4:00 na yamma, kuma har yanzu tana ci gaba da konewa zuwa lokacin rubuta wannan rahoto.

Ya ce, “A halin yanzu da nake magana da kai, ina iya ganin wutar tana ci gaba da konewa. Dukkan ginin mai bene biyu ya kama da wuta. Wannan gobarar ma ta fi wadda ta faru a kasuwar ƙasa da makonni biyu da suka gabata muni.”

I zuwa  lokacin da ake hada wannan rahoto, motar kashe gobara guda daya kacal aka gani a wurin da lamarin ya faru.

Kasuwar Singer ita ce mafi girman kasuwar kayayyaki a Kano da ma arewacin Najeriya, inda ake sayar da kayan masarufi da abinci zuwa yawancin jihohin arewa har ma da wasu kasashen makwabta na yammaci da tsakiyar Afirka.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker