Siyasa

INEC Ta Sanya 20 ga Fabrairu 2027 a Matsayin Ranar Zaben Shugaban Kasa

Hukumar zabe ta kasa ta ayyana ranar 20 ga Fabrairu, 2027 a matsayin ranar gudanar da zaben shugaban kasa na gaba.

Shugaban hukumar, Joash Amupitan, ya sanar da hakan ne yayin taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Juma’a.

Ya kuma bayyana cewa zaɓukan ‘yan majalisar tarayya za su gudana a ranar guda, yayin da zaɓukan gwamnoni da na majalisun dokokin jihohi za su gudana a ranar 6 ga Maris, 2027.

A cewarsa, hukumar ta kammala shirye-shiryen da suka dace domin tabbatar da gudanar da zabukan cikin tsari da nasara.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker