
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kammala komawa jam’iyyar APC a hukumance, bayan wani ƙaramar biki da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar.
Taron komawar ya samu halartar manyan jiga-jigan jam’iyyar APC, ciki har da tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje; Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Barau Jibrin; Sanata Kawu Sumaila; Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas; ƙaramin Ministan Gidaje, Abdullahi Ata, da sauran manyan baƙi.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa ya yanke shawarar komawa jam’iyyar APC ne bayan tuntuɓar abokan siyasa tare da la’akari da muradun ci gaban al’ummar Jihar Kano.
“Mun ɗauki wannan mataki ne domin Jihar Kano ta samu damar cin gajiyar manyan ayyukan ci gaba daga gwamnatin tarayya,” in ji gwamnan.
Ya ƙara da cewa akwai wasu muhimman damar da jihar ba ta cika amfana da su daga gwamnatin tarayya ba saboda bambancin jam’iyya, wanda hakan ya sa suka ga dacewar komawa APC domin amfanin Kano.
Gwamnan ya ce ya koma jam’iyyar APC tare da wasu daga cikin kwamishinoninsa, ƴan majalisar dokokin jihar, ciki har da Kakakin Majalisar, da kuma ƴan Majalisar Tarayya takwas.
Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa matakin ya samo asali ne daga gamsuwarsa da salon shugabanci da manufofin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, waɗanda ya ce suna da tasiri wajen bunƙasa ci gaban ƙasa baki ɗaya.





