Wani matashi dan jihar Delta zai aure mata biyu a lokaci daya
Matashin dai mai suna Samson Uthuko Uloho dan jihar Delta a kudan cin Nigeria ya shirya tsaf dan auran yan mata 2 a lokaci daya.
Wanda a halin yanzun har an sa ranar auren ranar a sabar 11 ga watan April 2021 a karamar hukumar Isoko ta kudu.
Sunayen yan matan kuwa sune Evelyn da Faith, tuni katin gayyatar daurin auren ya bazu a shafukan sada zumunta inda kowa yana tofa albarkacin bakin sa. Ga muharar shafin twitter akan wannan katin gayyatar wanda shafin wani mai suna @wakajugde ya wallafa.
Nobody do reach Isoko people…. Oga Samson dey marry on the 11th to 2 different women ๐๐พ pic.twitter.com/qJSzsumPBa
โ ๐๐ข๐ง๐ข๐ฌ๐ญ๐๐ซ Of Infrastructure ๐ซ๐ฎ (@wakajugbe) April 1, 2021
Wannan batu a arewancin Nigeria abune wanda matasan arewa sun jima da yin hakan kuma ya fara zama ruwan dare sai dai kudan cin Nigeria abune bako wanda ba’a saba yin sa ba.
Haka zalika a addinin kirista wannan batun babban lamarine dan kuwa auren mata biyu kamar haramun ne a garesu saidai gashi shi wannan matashi zai aure mata biyu a lokaci guda.