Kungiyar kare hakkin dan adam mai suna ππ’ππ’π³ππ§π¬ ππ§π’πππ ππ¨π« πππππ ππ§π πππππ’π₯π’ππ² (CUPS) ta ce tana cigiyar wani matashi mai suna Idiyo dan a kauyen KETAKO, AUDALLAWA a yankin Kafin Hausa na jihar Jigawan Nijeriya. Kungiyar ta yi zargin cewa matashi Idiyo ya yi wa wata yarinya mai shekaru 13 fyade kuma ta haihu a makon da ya gabata bayan ta yi fama da nakuda mai tsanani.
Shugaban kungiyar ta CUPS Dakta Idris Ahmed ya ce bayanan da suka samu sun ce matashin da ya yi wa yarinyar wannan aika-aika bai shiga hannun hukuma ba a saboda abin da ya kira gazawa ta βyan sandan Nijeriya.
A yanzu kungiyar CUPS neman bayanan da za taΒ tunkari kotu da su don ganin an kamo Idiyo wanda rahotanni ke cewa ya musanta cewa shi ya yi wa yarinyar fyade har ta samu ciki ta haihu.
Source: DCL Hausa