Labarai

Cutar koronabirus ya cika kwana 100.

A ranar 31 ga watan Disamba – kwana 100 daidai kenan – gwamnatin China ta bayar da rahoton gano wata cutar “murar mashako” wato koronabirus da ba a san kalarta ba ga Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO.

Wannan cutar dai ta zama annoba da ake kira da COVID-19 a yau.

Cutar dai an fara samun bullarta a birnin Wuhan dake birnin sin wato chaina, tuni ta karade sauran sassan duniya, inda mutum fiye da miliyan daya da rabi suka kamu da cutar sannan kuma kusan 90,000 suka mutu a sanadiyar cutar koronabirus.

Shugaban WHO, Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus ya tuna da wadannan kwana 100 na alhini a wurin taron manema labarai ranar Alhamis.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker