Siyasa

2027: Kansiloli 8,122 Sun Goyi Bayan Tinubu

Kungiyar Progressive Serving Councillors’ Forum of Nigeria ta bayyana goyon bayanta ga sake tsayawar takarar Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, a zaben 2027.

An cimma matsayar ne a taron hadin kai na kasa na kwanaki biyu da aka gudanar a Abuja ranar Laraba, inda sama da kansiloli 8,000 suka halarta.

Babban sakataren kungiyar, Adeoye Adeniyi daga Jihar Ondo, ya ce shawarar ba wai saboda jam’iyya ba ce, sai dai bisa la’akari da irin ayyukan da shugaban ya gudanar a fannoni daban-daban na tattalin arziki.

Ya kara da cewa wasu kansiloli daga sauran jam’iyyu suna tattaunawa da kungiyar domin su ma su mara wa Tinubu baya a zaben 2027.

A nasa bangaren, mai jagorantar taron, Ademola Abdulwakeel, ya ce an dauki matakin ne bayan tuntuba da masu ruwa da tsaki, yana mai cewa nasarorin shugaban kasa sun bayyana ga kowa.

Ya kuma ce taron ya taimaka wajen horas da kansiloli kan dabarun jawo kuri’u a matakin kasa da kasa, tare da kudurin yada manufofin gwamnati a matakai daban-daban.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker