Yanzu Yanzu : An sanya takunkumi a kananan hukumomi uku na Bauchi
Gwamna Bala Muhammad ya amince da sanya da takunkumi a kananan hukumomi Katagum, Giade da Zaki na tsawon kwanaki 10 a wani matakin yaki da yaduwar cutar corona.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da manema labarai kan karin masu dauke da cutar Covid 19.
Gwamnan yace takunkumin ya zama wajibi la’akari da hauhawar adadin masu dauke da cutar a kananan hukumomin.
A cewar sa, an samu sabbin rahotannin bullar cutar a jikin mutane arbain da hudu sakamakon yawan zirga zirgar wasu al’umar yankin zuwa jihohin dake fama da cutar.
Gwamna Bala yace gwamnati ta tattauna da shugabannin yankunan kafin sanya dokar tare da duba hanyoyin bada kariya wa al’umar jiha baki daya.
Yace a jiya asabar kadai, sakamakon gwaji ya nuna bullar cutar a Azare da Giade da Zaki sakamakon yawan tafiye tafiyen wasu daga cikin al’umar yankin zuwa garuruwan Hadeja, Kano da Jigawa.
Yace takunkumin na kwanaki goma zai bada dama wa kwamitin yaKi da cutar killace tare da jinyar wadanda suka harbu da cutar tare da gudanar da gwaji kan wasu.
Ya kara da cewa gwamnatinsa zata dauki sabbin matakan yaKi da cutar Covid 19 ta hanyar fadada gwaji kan cutar.
Ya sanar da cewa gwamnatinsa da hadin guiwar Babban Bankin Kasa CBN ta samar da wadatattun gadaje a asibitin FMC dake Azare don jinyar marasa lafiya.
Gwamna Bala ya kara da cewa gwamnatin jiha za ta hada kai da takwararta ta Pilato don saukaka gwaji kuma akan lokaci.
Har wa yau gwamnan ya umurci mataimakin sa Sanata Baba Tela da ya koma Azare don sanya ido kan lamuran yaKi da cutar.
Shima Sanata Baba Tela wanda har wa yau shine shugaban kwamitin yaKi da yaduwar cutar corona a jiha ya bayyana cewa daga ranar talatar me zuwa dokar takunkumin zata fara aiki a wuraren da cutar tayi kamari.
Lawal Muazu Bauchi
Me tallafawa Gwamna Bala Muhammad kan kafafen yada labarai na zamani
10 Mayu, 2020.