Yadda Ƴan Bindiga Suka Kashe Mutum 21 a Harin Ramuwar Gayya a Katsina

Akalla mutum 21 ne suka rasa rayukansu sakamakon wani hari da ƴan bindiga suka kai a yankin Tafoki da ke ƙaramar hukumar Faskari a jihar Katsina.
Shugaban ƙaramar hukumar Faskari, Surajo Aliyu Daudawa, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira da BBC, inda ya bayyana cewa harin ramuwar gayya ne bayan kashe wani ɗan bindiga, duk da cewa an cimma yarjejeniyar sulhu da su kusan watanni biyar da suka gabata.
Daudawa ya ce mazauna yankin sun wayi gari cikin tashin hankali bayan harin, yana mai jaddada cewa yankin bai fuskanci wata matsala ta tsaro ba tun bayan kulla yarjejeniyar sulhun da ƴan bindigar.
Ya bayyana cewa adadin mutanen da aka kashe ya kai 21, yayin da babu rahoton sace kowa a yayin harin.
Shugaban ƙaramar hukumar ya ƙara da cewa rahotanni sun nuna cewa ƴan bindigar sun yi yunkurin tafiya da mata, sai dai shugabanninsu suka hana hakan, suna cewa ba sace-sace suka zo yi ba, illa ɗaukar fansa.
Game da dalilin sake tasowar rikici bayan an yi sulhu, Daudawa ya ce kwanaki biyar kafin harin an samu rahoton sace mutane biyu tare da kwace babur guda ɗaya. A cewarsa, an bi tsarin yarjejeniyar sulhu ta hanyar tuntubar ƴan bindigar domin su taimaka wajen bincike.
Daga baya, an gano cewa mutanen biyu suna gidajensu, amma an tsinci gawar ɗaya daga cikin ƴan Fulani dajin da suka je taimaka wajen neman mutanen, lamarin da ake zargin shi ne ya haddasa harin ramuwar gayya.
Ya ƙara da cewa an riga an yi jana’izar mutanen da suka mutu a garin Doma, yayin da al’ummar yankin ke kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ɗauki tsauraran matakai domin hana sake faruwar irin wannan hari, musamman bayan ƙoƙarin dawo da zaman lafiya ta hanyar sulhu.





