Sanannen jarumi mai tasowa a masana’antar Kannywood, Sahir Abdoul wanda aka fi sanin sa da Malam Ali a cikin shirin Kwana Casa’in na gidan Talabijin na AREWA24 ya auri wata dattijuwa ‘yar kusan shekaru 60.
Wata majiyar sirri ‘Gulma da Dumi Duminsa’ ta bankado tare da watso hotunan bikin Jarumin da wannan Hajiyar wadda ake ganin aka yi bikin su a sirrance don gudun bakin jama’a ganin cewa haife sa. Lallai soyayya da dadi kuma babu ruwansa da tsufa.
A ranar 11 ga watan Janairun wannan shekaran ne dai Jarumin ya wallafa hotonsa da matarsa ta farko, inda ya raka hotunan bikinsu da sako cewa, ” Na kira ta da matar Aljanna. Allah ya miki albarka yadda kika kaunace ni domin Allah kema Allah ya kaunace ki ya kula da ke Amin” Manuniya ta ruwaito”. Bai jima ba da ya yi auren farko.
Yanzu dai hotunan auren jarumin da Hajiya ya fara bazuwa a kafafen sadarwa na zamani.