Labarai

Rundunar Yan sanda sun samu nasarar Hallaka Yanta’ada da ke dauke da muggan makamai acikin mota kirar Corolla mai lamba SRP-702XA Niger

Rundunar Yansandan Jahar Zamfara ta Samu Nasarar Halaka wasu Yanta’ada da suke dauke da muggan makamai acikin wata mota mai kirar corolla mai lamba SRP-702XA Niger.

Mun samu wannan labarin a shafin Hudu Yawa Babban mai taimakawa gwamnan jihar zamfara Bello Matawalle Maradun akan Sabbin Kafafun sada zumun ta na zamani yana cewa:

Wanna lamari ya faru Jiya Asabar da misalin karfe 12:15pm na rana ‘Yan sandan jihar Zamfara suka kwanta ma wasu rikakkun barayi masu garkuwa da mutane wadanda suka kware sosai wajen shigar da makamai zuwa ga ‘yan ta’adda

Barayin sun kwaso makamai a cikin mota daga jihar Taraba zasu kai Zamfara, sun iso hanyar garin Gummi zuwa Anka na jihar Zamfara ‘yan sanda suka musu harin kwanton bauna, biyu daga cikin barayin sun isa lahira babu shiri
‘Yan sanda sun samu motar barayin kirar Corolla mai launin baki tare da Registration number kamar haka: NIGER SRP 702 XA, da harsashin bindiga kusan guda 400, an samu makamin roka guda ukk, da bama-bamai guda biyu da harsashin bindiga mai jigida, sai kuma kayan tsafi.
Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker